Connect with us

News

Wata tsohuwa ‘yar kasar Uganda mai shekaru 70 ta haifi tagwaye

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wata tsohuwa ‘yar kasar Uganda mai shekaru 70 ta haifi tagwaye bayan da ta samu juna biyu ta hanyar ƙyanƙyashe ƙwai a dakin bincike kafin a dasawa mace a mahaifa (IVF) inda ta zama mace mafi tsufa a Afirka da ta haihu, kamar yadda asibitin da ta haifi jariran ya bayyana.

Cibiyar kula da lafiyar mata ta ƙasashen duniya da cibiyar haihuwa da ke Kampala babban birnin Uganda, ta ce Safina Namukwaya ta haifi namiji da mace.

Advertisement

Kotun daukaka kara Tace Zaɓen Dan Majalisar Kunchi/Tsanyawa Bai Kammala ba

“Wannan ba abu ne kaɗai ya yake nuna ci gaba a fanni likitanci amma harda nuna jajircewa na ɗan Adam,” in ji asibitin a shafin Facebook, biyo bayan nasarar haihuwa da Namukwaya ta yi ta tiyata a ranar Laraba.

Bbc ta ruwaito cewa Namukwaya ta shaida wa gidan talabijin na NTV mai zaman kanta cewa wannan ne karo na biyu da ta haihu cikin shekaru uku, bayan ta haifi yarinya a shekarar 2020.

Advertisement

Ta kara da cewa ta fuskanci matsaloli da dama a lokacin da take dauke da juna biyu, ciki har da rabuwa da mahaifin yaran.

“Maza ba sa son jin kina dauke da cikin tagwaye, tun lokacin da aka shigar da ni a nan mijina bai taba zuwa ba.”

Advertisement

Namukwaya ta ce ba ta san yadda za ta yi renon yaran ba, amma ta yi farin ciki da samun su bayan shekaru da dama da suka sha fama na rashin haihuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending