Connect with us

News

Za A Fara Yi Wa Masu Fyaɗe Dandaƙa A Jihar Kaduna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Gwamnatin Kaduna ta jaddada matsayinta na yin dandaka ga duk namiji ko macen da aka kama ya aikata fyade a jihar.

Kwamishinar Kyautata rayuwa ta jihar, Rabi Salisu ta ce wannan horo ne domin kawo karshe fyade daga kowane jinsi a jihar.

Advertisement

Hakkokin Talaka Da Suka Wajaba A Kan Shugabanni -Malam Ja’afar

Aminiya ta ruwaito cewa hukuncin yin dandaka ga maza da mata masu aikata fyade ya yi daidai da dokar jihar na yaki da cin zarafi na 2018.

Kwamishinar ta ce gwamnatin jihar yi dokar ta dandaka ce bayan tuntuban hukumomi da bangarorin da abin ya shafa da kuma wayar da kan al’umma kan illolin fyade.

Advertisement

Ta sanar da hakan ne bayan taron masu ruwa da tsaki da ma’aikatar ta gudanar ranar Alhamis da hadin gwiwar cibiyar inganta lafiya ta bai-daya (CIHP).

Babban jami’in CIHP, Dokta Austin Azihaiwe, ya ce taron na da muhimmanci lalubo hanyoyi da dabarun domin samun nasara wajan yaki da matsalar cin zarafi a cikin al’umma.

Advertisement

A wani labarin kuma Hakkokin Talaka Da Suka Wajaba A Kan Shugabanni -Malam Ja’afar

Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi gargaɗin cewa dole Isra’ila ta dauki kwakkwarar mataki wajen tabbatar da kare fararen hula a Gaza kafin ta sake kai hare-hare Gazan.

Advertisement

Antony Blinken wanda ke ziyara a yankin, ya ce Isra’ila wadda ke ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da kwararrun sojoji a duniya, na da damar samun nasara a kan Hamas, to amma dole ta yi taka tsan-tsan don kaucewa cutar da fararen hula.

Nan ba da jimawa ba ne kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a Gaza za ta zo karshe.

Advertisement

Hiba Husseini Lauya ce da ta taɓa shiga yarjejeniyar Isra’ila da Falasɗinu a 1994, ta ce ‘ba abu ne na dogon lokaci ba, ina nufin babbar manufar dukkan bangarorin a kan wannan yarjejeniya ita ce don a saki fursunoninsu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending