News
Sojojin Isra’ila Sun Kashe Falasdinawa 240 Sun Jikkata 650 A Gaza
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumoni a Zirin Gaza sun ce Falasdinawa 240 Isra’ila a kashe, ta kuma jikkata wasu 650 daga ranar Juma’a.
Hukumar Hamas ta ce Isra’ila ta kai hare-hare sama da 400 da jirage da kuma ta kasa a sassan Gaza tun bayan karewar wa’adin tsagaita wuta da bangarorin suka yi.
Mai Tura Baro Ya Kashe Wani Mai karɓar Haraji Kuma Ya Kashe Kansa
Hamas ta ce sojojin Isra’aila sun tsananta hare-hare a sassan yankin Khan Younis da ke Kudancin Zirin Gaza inda suka rika rusa gidaje da mutane a cikinsu.
Tun bayan karewar wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutan mako guda da Hamas da Isra’ila suka cim-ma, sojojin Isra’ila suka rika ragargazar yankunan Gaza.
Akasarin wadanda hare-haren Isra’ila yi ajalinsu a Gaza dai kananan yara ne da tsofaffi da kuma mata.
A kimanin wata biyu da Isra’ila ke ragargazar Gaza, yawan Falasdinawan da ta kashe sun haura mutum dubu 15.
A wani labarin kuma Mai Tura Baro Ya Kashe Wani Mai karɓar Haraji Kuma Ya Kashe Kansa
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
