Connect with us

News

Mai Tura Baro Ya Kashe Wani Mai karɓar Haraji  Kuma Ya Kashe Kansa

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

 

Advertisement

Ruɗani ya bayyana a garin Benin yayin da wani mai Baro da har yanzu ba a san daga ina yake ba ya kashe wani mai karɓar haraji kuma ya kashe kansa.

Wikki Time ta ruwaito cewa Lamarin dai ya faru ne a jiya Juma’a a titin Mission, dakewa ƙaramar hukumar Oredo ta jihar Edo.

Advertisement

RANAR CUTAR KANJAMAU TA DUNIYA: Sama da mutum 4000 da ke ɗauke da cutar a Kano dake amsar magani kyauta a asibitocin jihar

Al’amarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna yankin da ma masu shaguna inda suka yi gaggawar rufe shagon su saboda tsoron kada a kai musu hari.

Ce-ce-ku-ce ne ya shiga tsakanin mai tukin baro da mai karbar harajin inda mai tura baro ya yi taurin kai yaƙi biyan harajin naira 50 na ranar.

Advertisement

An tattaro cewa abin da ya fusata faruwar lamarin, shi ne mai karbar kudaden ya fusata ya hamɓarar da baron ɗauke da buhunan kayayyaki inda ya faɗi gefen titti kayan ciki suka faɗin wanda hakan ya haifar da musayar kalamai a tsakaninsu inda sakamakon haka mai tuka keken ya fito da wuka daure a kugu ya daɓa wa mai karbar harajin.

Ƙokarin jama’a wajen ganin an daƙile harzuƙan mai baro ya ci tura domin sai da ya tabbatar mai harajin ya mutu.

Advertisement

Mai tura Baron, bayan ya tabbatar da cewar mai karɓar harajin ya mutu, shi ma ya daɓa wa kansa wuka a wuyan saboda ya san cewa mutanen wurin ba barinsa za su yi ba.

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun SP Chidi Nwanbuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending