Connect with us

News

Tallafi Ya Kamata A Dinga Baiwa Ɗalibai Ba Bashi Ba – ASUU

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jihar Bauchi, ta bayyana aniyar ta na ƙin amincewa da bashin da gwamnatin tarayya ta ayyana zata baiwa dalibai domin tallafawa karatun su.

Ko’odinetan kungiyar ta ASUU shiyyar jihar Bauchi, Farfesa Lazarus Maigoro shi ne ya bayyana haka a jiya a wajen bikin bayar da tallafin karatu ga dalibai marasa galihu su 19 daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi.

Farfesa Maigoro ya ce, “Tambayar a nan ita ce: Wa ye zai biya bashin? Menene makomar waɗanda ba za su iya biya ba? Tashin hankali da ɗalibai za su fuskanta saboda bashin da suka karɓa ka iya hana su karatu .

“Tunanin cewa za su kammala karatu da bashin Naira miliyan 4 ko fiye da haka a kansu ba tare da sanin mafitar yadda za su iya biya ba, haka wani nau’in baraza na ne ga rayuwar su.

A wani labarin kuma Nijeriya ta bukaci sojojin Jumhuriyar Nijar su bar Bazoum ‘ya koma wata kasa’

Advertisement

Ma’aikaatar tsaron Birtaniya ta aike wani jirgin leen asiri domin samo mata bayanai kan inda Hamas ke tsare da fursunonin da suka yi garkuwa da su.

Sakatariyar Lafiya Victoria Atkins ta shaida wa BBC a ranar Lahadi cewa “jiragen ba ma su makamai ba ne” kuma BBC ta tabbatar da haka daga Ma’aikatar tsaro.

Ta ce : “Suna neman waɗanda aka yi garkuwa da su ne, duk da cewa an saki wasunsu amma har yanzu akwai waɗanda ke hannu da ake buƙatar su kubuta suma.”

Akwai ‘yan Birtaniya biyar da suka ɓata tun bayan fara rikicin Hamas da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

 

 

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending