News
Najeriya Za Ta Tura Jirage Marasa Matuka A Kan Iyakokin Kasar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta ce za ta fara amfani da jirage masara matuka wajen yin sintiri a kan iyakokin kasar.
Kwamturola-Janar ta hukumar, Caroline Wura-Ola Adepoju, ta ce tuni Gwamnatin Tarayya ta fara tattauna da kamfanin samar da na’uori na Huawei da ke kasar China kan samar da fasahar na’ura wajen sintiri a kan iyakokin Najeriya.
Ta sanar da haka ne a taron Ranar ’Yan Gudun Hijira ta Duniya a ranar Talata.
Game da fargabar ’yan Najeriya kan yiwuwar harin kuskure irin wanda jirgin soja mara matuki ya kai wa masu taron Mauludi a Kaduna, shugabar hukumar ta ba da tababcin cewa babu wata matsala da za a samu wajen amfani da jirage marasa matuka a kan iyakokin kasar.
Aminiya ta ruwaito cewa ewa za a yi amfani da jirage marasa matuka a kan iyakokin kasar ne kawai wajen tattara bayanai kai-tsaye.
A wani labarin kuma Hukumar INEC ta Rantsar da Sabbin Kwamishinonin Zaben Tara
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
