Connect with us

News

Hukumar INEC ta Rantsar da Sabbin Kwamishinonin Zaben Tara

Published

on

Shugaban Hukumar zabe Mai Zaman Kanta ta kasa Farfesa Mahmoud yakubu

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Shugaban Hukumar zabe mai zman kanta ta kasa INEC Farfesa Mahmoud yakubu ya rantsar da sabbin shugabannin Hukumar a shelkwatar Hukumar zabe Dake birnin tarayya Abuja

Farfesa Mahmoud yakubu ya rantsar dasu awani taro irinsa na farko tun Bayan kammala zaben Jihohin Kogi-Bayelsa- Da jihar Imo.

Sake Fasalin Kudi Da Gwamnatin Da Ta Shude Tayi Ya Durkusar Da Harkar  Manoma A Najeriya

Shugaban kasa Bola Ahmad tunubu shine ya nada shugabannin Guda Tara bayan majalisar dattawan Nigeria ta amince dasu, duk da kalubalantar matakin Hakan Ga wasu kungiyoyin Nigeria sukayi

Ana zargin cewa akwai wasu daga cikin wadanda Shugaban kasar ya nada Yan jam’iyyar APC ne Wanda Hakan ya Saba da doka acewar kungiyoyin

Advertisement

Punch Ta rawaito Cewa Bayan rantsar dasuda Farfesa Mahmoud yakubu yayi Tuni ya turasu jihohin Kebbi, Borno, Edo, Akwa Ibom, Kaduna, Kwara, Ondo, Ekiti, da jihar Nasarawa

A wani labarin kuma Sake Fasalin Kudi Da Gwamnatin Da Ta Shude Tayi Ya Durkusar Da Harkar  Manoma A Najeriya

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending