Connect with us

News

Hukumar INEC Za Ta Gudanar Da Zaɓukan Cike Gurbi A Watan Fabarairu 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Hukumar zaɓe mai zman kanra ta kasa Inec, ta ce tana duba yiwuwar gudanar da zaɓukan cike gurbi da kuma sake zaɓuka a wasu wuraren ranar 1 ga watan Fabarairu domin cike guraben da ake da su a majalisun dokoki na jiha da na tarayya.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wani taro da shugabannin jam’iyyu gabanin zaɓukan.

Rundunar Soji sun ceto mutum 13, sun kama wasu 11 da ake zargi da bai wa ‘yan ta’adda kayayyaki a Zamfara

Yakubu ya ce a ƙarshen shari’oi kotuna sun umarci Inec ta gudanar da zaɓen cike gurbi a mazaɓu 34 na jihohi, da kuma tarayya da suka haɗa da ɗaya a majalisar dattawa, sai mazaɓun tarayya 11, da mazaɓun jihohi 22.

Shugaban Inec ya ce hukumar za ta gudanar da zaɓukan ne sakamakon gurbin da aka samu sanadin ajiye aiki ko kuma mutuwa.

Bbc ta ruwaito cewa  za a saki jadawalin zaɓen da kuma ranar da za a yi a ƙarshen taron da shugabannin jam’iyyu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending