Connect with us

News

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a JAMB ta kara kuɗin fom

Published

on

Masu Zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, UTME
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a, JAMB, ta kara kudin rajistar jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare, UTME, ta 2024 da ke tafe, UTME, inda ta kuma sanar da bude shafin yin rajista na yanar gizo don saka bayanan masu yin rijista.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a jiya Lahadi, hukumar ta ce wadanda za su zana jarabawar ta gwaji za su biya Naira dubu 7,700, yayin da wadanda ba su da sha’awar zana jarabawar gwajin za su biya Naora dubu 6,200.

An ci tarar JoseMourinho da Roma Yuro 40,000 saboda sukar alkalin wasa.

Sai dai jaridar DAILY NIGERIAN ta lura da karin Naira 2,100 a cikin kudin jarabawar bana domin a shekarar da ta gabata wadanda suka zana jarabawar sun biya Naira 5,600 ne kacal.

Sanarwar ta ce: “Muna masu sanar da duk masu neman jarrabawar UTME/DE ta 2024 cewa an bude shafin bayar da bayanai na masu son zama jarrabawar a hukumance, yayin da za a fara siyar da gubdarin don din a ranar Litinin 15 ga Janairu, 2024.

Advertisement

“Don haka, yana da muhimmanci ku kiyaye ranakun da za a zana jarabawar UTME/DE mai zuwa kamar yanda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito 

A wani labarin kuma An ci tarar JoseMourinho da Roma Yuro 40,000 saboda sukar alkalin wasa.

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Advertisement

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending