Connect with us

News

Yadda Shugaba Tinubu Ya Sasanta Rikicin Siyasar Jihar Rivers

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar kawo karshen fitinar da ta kaure a jihar Rivers tsakanin gwamnan Mista Fabura da magoya bayan tsohon maigidansa tsohon gwamna Nyelson Wike, wanda kuma shi ne ministan babban birnin tarayya.

Rikicin siyasa da ya bullo a jihar Rivers tsakanin gwamnati mai ci da kuma magoya bayan tsohuwar gwamnati, ya dauki hankali a fadin Najeriya, lamarin da ya sa shugaban kasa gayyatar dukkan bangarorin domin zaman sulhu.

Akalla Mutum 250,000 sun tsere daga gidajensu sakamakon rikici a jihar Al Jazirah ta Sudan

Halin da ake ciki dai za a iya cewa an cimma matsaya a taron, inda dukkan bangarorin da aka gayyata suka tattauna tare da samar da wasu sharudda da ake sa ran za su tabbatar da zaman lafiya.

Cikin sharuddan da aka samar, ‘yan majalisa da suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC maimakon a kore su za su koma bakin aikinsu a Majalisa. Haka kuma yunkurin tsige gwamna da Majalisar ta fara za ta dakatar da shi.

Advertisement

Haka kuma an cimma matsayar cewa kwamishinoni da suka ajiye aiki za su koma bakin aiki. Shi kuma gwamna Mista Fabura zai sake aikawa Majalisa kasafin kudin da suka ki kulawa.

A wani labarin kuma Akalla Mutum 250,000 sun tsere daga gidajensu sakamakon rikici a jihar Al Jazirah ta Sudan

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Advertisement

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending