Connect with us

News

Bai Kamata Gwamnatin Jihar Kano Ta Ɗauki Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi Ta Gina Gadoji A Birni Ba -Abba Hikima

Published

on

Abba Hikima Fagge
Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Lauyan nan na Kano, Abba Hikima Fagge, ya bukaci Gwamnatin Kano da ta duba Allah ta tsayar da aikin gadojin da ta kuduri aniyar yi a Kano ta hanyar ɗibar kudaden kananan hukumomi don gina gadoji a birni alhali kauyuka na cikin matsanancin hali da bukatar aiki.

Abba Hikima ya bayana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Laraba inda mabiyansa ke ci gaba da bayana tsokacinsu kan kalaman nasa.

Kotu ta haramta wa Donald Trump tsayawa takara a 2024

Hikima ya ce, “Irin wadannan abubuwan da ake dauko wa ke sawa mutane suke daukar gaba daya ashe ‘yan siyasa irinsu daya, ”

Leadership ta ruwaito cewa Takardar da aka fitar don fitar da kudaden kananan hukumomi don gina gadar Dan Agundi

Advertisement

Takardar da aka fitar don fitar da kudaden kananan hukumomi don gina gadar Dan Agundi

“Yanzu saboda Allah ina adalci anan? Kauyukan Kano suna cikin mugun hali, kwanaki Freedom Radio ta yi ta bankado matsalolin kauyukanmu amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya Me wannan kudin?”

“Lallai akwai wani abu da yake faruwa a kasa.” cewar Abba Hikima.

A Wani labarin kuma Masu shayi koko da kosai na zabga ciniki a garin Kano a dalilin yanayi na hunturu da aka shiga.

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Advertisement

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending