Connect with us

News

Emefiele Ya Musnta Zargin Rahoton Mai Bincike Na Musamman Kan Bankin Kasa CBN

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN Emefiele, ya musanta rahoton da babban mai bincike na babban bankin, Jim Obazee, ya bayar na cewa ya ajiye kudi fam milliyan 543 da dubu 482 da 213 a bankunan kasar Birtaniya da sauran su ba tare da izini ba.

Emefiele, wanda aka saki daga gidan yarin na Kuje a karshen mako, ya bayyana hakan ne a daren jiya a cikin wata sanarwa, inda ya bayyana rahoton a matsayin yaudara da kuma kididdigar kokarin da ake yi na cutar da shi da kuma biyan bukatar son kai ta mai binciken.

Advertisement

Kurmawa Special Primary School Na Gayyatarku Taron Tsofaffun Dalibai Da Ta Saba Duk Shekara

Ya ce sassan da abin ya shafa na CBN suna da hurumin gudanar da irin wadannan ayyuka kamar yadda doka ta tanada a cikin CBN.

Emefiele ya nunar da cewa ya umarci lauyoyinsa da su fara aikin shari’a don wanke sunansa daga maganganun batanci da ke kunshe a cikin rahoton

Advertisement

A wani labarin kuma Kurmawa Special Primary School Na Gayyatarku Taron Tsofaffun Dalibai Da Ta Saba Duk Shekara

Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.

CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.

Advertisement

“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.

“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”

Advertisement

Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.

Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending