Connect with us

Sports

ƴan wasan Gombe United sun dawo gida a motar haya bayan da motarsu ta lalace

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Gombe United Mohammed Babaganaru ya soki yadda kungiyarsa ke zuwa wuraren buga wasa a wajen gida makare, yana mai bayyana lamarin a matsayin “abu maras dadi” saboda yadda ya ke taɓa kwazon kungiyarsa.

Babaganaru ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai jim kadan bayan kammala wasan mako 15 na gasar Premier ta Najeriya (NPFL) 2023/2024 da aka buga a filin wasa na Pantami Township, Gombe.

Advertisement

Emefiele Ya Musnta Zargin Rahoton Mai Bincike Na Musamman Kan Bankin Kasa CBN

Gombe United ta lallasa Katsina United da ci daya mai ban haushi a minti na 76 da fara wasa ta hannun dan wasan gaba na Gombe, Mujeeb Odufeso.

Babaganaru ya danganta nasarorin da kungiyarsa ta samu a baya-bayan nan da sauye-sauyen na dabaru da aka yi wa kungiyar ba wai kudi ba.

Advertisement

Kungiyar ta samu nasara a wasanni biyu ta kuma yi kunnen doki daya a wasanni ukun da ta buga.

Ya ce yana rokon gwamnati ta kawo musu kayan agaji. Yawancin lokaci, suna tafiya ne a makare, wani lokacin kuma suna zuwa garin da za su yi wasan a ranar wasan wanda ba ya basu damar hutuwa kafin fara wasan

Advertisement

Wikki Time ta ruwaito cewa Babaganaru ya ce ya yi alkawarin Zai ci gaba da kira ga gwamnati da ta taimaka masu saboda suna bukatar taimakon kudi

Ya ce sai da suka yi hayan motocin bas domin dawowa gida Gombe, bayan da motarsu ta lalace a Akure.

Advertisement

Sannan ya yi kira ga magoya bayan kungiyar da su ci gaba da ba kungiyar goyon baya da kuma yi wa kungiyar addu’a domin kungiyar na aiki tukuru domin ganin ta faranta musu rai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending