News
Kwana 7 Na Kasa Barci Saboda Jiran Hukuncin Kotun Koli —Bala Mohammed
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya ce kwana bakwai ya kasa barci saboda jiran hukuncin Kotun Koli kan zabensa.
Bala Mohammed ya shaida wa magoya bayansa cewa, “Barci ya gagare ni ne saboda kullin da wasu tsofaffin shugabannin jihar suka je suka yi a fadar shugaban kasa da nufin a kwace kujerata.
Hotuna: Yayin Da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ke Kan Hanyarsa Ta Jihar Kano
“Sun shaida wa fadar shugaban kasa cewa ni matsala ne, kuma zan kara zame musu babbar matsala idan na ci gaba da zama Gwamna, amma cikin ikon Allah mun yi duk mai yiwuwa, kuma mun yi nasara a Kotun Koli.
“Sun je sun kulla makirci don shiga tsakanina da abokina, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da ma shi kansa Shugaba Tinubu, duk da cewa yana yabawa da ayyukan da muka yi a jihar,” in ji shi.
Hotuna: Yayin Da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ke Kan Hanyarsa Ta Jihar Kano
Gwamna Bala ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu kan rashin tsoma baki a harkokin shari’a, lamarin da ya haifar da hukuncin da aka yanke ranar Juma’a.
Aminiya ta ruwaito cewa Kotun koli bisa adalcinta ga dukkan kararrakin da aka shigar a gabanta, inda ya ce hukunce-hukuncen na ranar Juma’a sun dawo da martabar bangaren shari’a a matsayin matakin karshe na share hawayen talaka.
Daga nan sai ya ce yanzu abin da zai fi mayar da hankali a kai shi ne yi wa al’umma aiki tukuru da kuma samo wanda ya cancanta da zai maye gurbinsa, ya kuma yi wa al’umma aiki fiye da shi.
A wani labarin kuma Hotuna: Yayin Da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Ke Kan Hanyarsa Ta Jihar Kano
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
