Mazauna ƙauyen Nahuta da ke cikin Ƙaramar Hukumar Batsari a Jihar Katsina, sun fice daga garin ba shiri, bayan ‘yan bindiga sun afka wa sansanin sojojin da ke kusa da su, an yi gumurzun yaƙi.
Lamarin ya faru ranar Lahadi ɗin nan da dare, inda wata majiyar cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun zarce 100 waɗanda suka afka wa sansanin na su wajen 11 na dare.
Yadda Tsohon Minista Ya Jagoranci Tattara Miliyan N50 Kudin Fansa Ga ‘Yan Matan Da Aka Sace
A artabu da gwagwagwar da suka yi, ‘yan bindigar sun banka wa motocin sojoji biyu wuta. Amma dai majiyar wadda ta roƙi a ɓoye sunan ta, ta ce ba a kashe soja ko ɗaya ba.
“Kai, lamarin fa ya yi muni sosai, saboda ‘yan ta’addar sun ajiye baburan su can nesa da sansanin mu, sannan suka yi mana tattaki a ƙasa, wajen ƙarfe 11 na dare. Kawai sai muka riƙa jin harbi na tashi daga yammacin mu. Hakan ya nuna mana abokan aikin mu da ke daidai wurin su na cikin babban hatsari kenan.
“Can a ƙarshen sansanin suka fara kai hari. Ni da abokan aiki na muka yi kwaton shirin artabu, muka yi ta darzaza masu ruwan wuta. To abin ka da sarkin yawa, ‘yan bindigar sun fi mu yawa, kuma sun kasu gida uku,” cewar majiyar mu ta cikin sojoji.
Soja mai ba PREMIUM TIMES lahari ya ƙara da cewa sun ja da baya don kada ‘yan bindigar su karkashe su bayan da ‘yan bindigar suka danna cikin sansanin na su.
Ya ƙara da cewa a gaskiya sansanin su na buƙatar ƙarin makamai da albarusai domin cika-aiki.
Bayan kai wa sansanin sojojin farmaki, ‘yan bindiga sun kutsa cikin garin Nahuta, amma suka samu kowa ya gudu.
“Ai mu dai ko da muka ji ruwan harbe-harbe, sai duk muka tsere cikin daji,” cewar wani mazaunin garin Nahuta, wanda shi ma ya ce kada a bayyana sunan sa.
Daga nan ‘yan bindiga sun riƙa fasa kantina su na kwasar kayan abinci da kayan masarufi. Kuma sun kwashi tumakai, sun kuma kashe shanu da dama.
Amma dai har lokacin rubuta wannan labarin babu rahoton rasa ran wani mazaunin garin Nahuta. Hakan ya sa aka riƙa zaton cewa ‘yan bindigar sun kai hari ne kawai don su saci kayan abinci su koma cikin daji.
Wakilin PREMIUM TIMES ya ga mutanen
garin suna hijira zuwa cikin Batsari da Wagini, garuruwan da ake ganin su akwai sauƙi-sauƙin matsalar tsaro.
Yawancin masu gudun hijirar sun ƙi yarda su yi magana da wakilin mu. Amma wata mata mai suna Nana Nafisa, wanda ke ɗauke da buhu, kuma ta na riƙe da hannun ƙaramar yarinya, ta ce ita Batsari za ta koma ta yi zaman gudun hijira a can.
“Sojoji dai na bakin ƙoƙarin su a gaskiyar magana,” inji ta. “Duk mun san su na ƙoƙarin kare mu. Amma gaskiya lamarin da ya faru jiya kam na daban ne. Yau dai kam ba zan iya kwana garin nan ba.”
Wata mai suna Maryama kuwa ta shaida wa wakilin mu cewa ta na tsakar barci, “sai na ji miji na ya na ce min tashi! Na zabura ɓigit, na shiga ɗakin yara na ɓoye,” inji ta.
Ta ce ‘yan gidan su baki ɗaya duk sun gudu zuwa cikin Batsari.
Wakilin PREMIUM TIMES ya kira lambar Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Katsina, Abubakar Sadik-Aliyu da ta Kakakin Runduna ta 17 ta Sojojin Najeriya da ke Katsina, Oliza Ethinlaiye, kuma ya tura masu saƙon tes, amma ba su amsa kira ba, kuma ba su maida amsa saƙon tes ba.
