News
Wasu Mutane ‘Yan Kalilan Ne Suka Wawure Arzikin Najeriya Ta Hanyar Tallafi – Shugaba Tinubu
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Shugaba Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa wasu tsirarun mutane ne suka sace mulkin Najeriya da sunan tallafi a cikin shekaru 40
Tinubu, ya koka da yadda ‘yan Najeriya ke fama da radadin abin da ya faru
Tashin farashin kayan abinci ya tilasta yawancin magidanta kasa ɗora tukunya sau uku a rana
A cewar shugaban yana yin duk mai yiwuwa dan ganin ‘yan Najeriya sun kasance cikin walwala
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana a ranar Litinin cewa wasu tsirarun mutane ne suka sace mulkin Najeriya da sunan tallafi a cikin shekaru 40 da suka gabata.
Tinubu, ya koka da yadda ‘yan Najeriya ke fama da radadin abin da ya faru.
Daily Post ta ruwaito cewa da yake jawabi a wajen bikin rantsar da Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo karo na biyu a Owerri, Shugaban kasar ya ce ya san halin da ‘yan kasa ke ciki, yana mai ba su tabbacin cewa ana fuskantar kalubalen da muhimman sauye-sauyen suka kawo.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta kara ba da kulawa ga ilimi da kiwon lafiya, tare da samar da hanyoyin bunkasa masana’antu da saka hannun jari bisa manufarsa ta samar da kasa mai kwanciyar hankali.
A cewar Tinubu: “A cikin shekaru 40 da suka wuce, wasu ‘yan tsirarun mutane ne suke sace mulkin kasar mu suna kiranta tallafin, amma na kira ta a banza.
“A yanzu, dukkanmu muna jurewa kuma muna raba wannan ciwo. Amma abubuwa suna kallo. Al’amura za su yi kyau ga dukkan ‘yan Najeriya. Tare da ni, akwai bege.
“Ina tabbatar muku cewa za a sami ci gaba mai yawa a fannin ilimi ga ‘ya’yanku; fifikon masana’antu kuma kiwon lafiya zai sami karin kaso da kulawa. Za mu horar da karin ma’aikatan lafiya.”
A wani labarin kuma Tashin farashin kayan abinci ya tilasta yawancin magidanta kasa ɗora tukunya sau uku a rana
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
