News
Shugaban Tunubu ya Jinjnawa Buhari sabida Rashin Yin Katsalandan Cikin Gwamnatinsa.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunubu ya Jinjnawa Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sabida Rashin Yin Katsalandan Cikin Gwamnatinsa.
Bola Ahmad Tunubu ya Bayyana Hakan yau a Birnin Tarayya Abuja yayin Kaddamar da Littafin da Femi Adesina ya Rubuta akan Jagorancin Buhari
An Tarwatsa Mutane Daga Garuruwa Sama Da 335 Tsakanin 2017 Zuwa 2024 A Jihar Neja
Tunubu ya Kara da Cewa Tun Lokacin da Buhari ya Mika masa Ragamar Shugabancin Ƙasar Nan, Bai taba Nuna Bukatar baiwa Wani Mukami Cikin Tsofaffin Jami’an da suka Yi Aiki dashi
Rahotanni na nuni da cewa Wannan shine Karon Farko da Shugabannin suka Hadu a bainar Jama’a Tun Bayan Da Suka Sanya hannun wajen Mika Mulki da karba.
Haka Kuma Jaridar Inda Ranka ta rawaito Cewa Tsohon Shugaban Kasa na Mulkin sojoji Yakubu gawon da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osingbanjo da uwargidan Tsohon Shugaban Aisha Buhari da sauran Tsofaffin Mukarraban Gwamnatin Tsohon Shugaban Kasar duka sun Halacci Bikin Kaddamar da Littafin
