Connect with us

News

Bom ya tashi da wasu ‘Almajirai’ masu karatun islamiyya, ɗaya ya rasu, 10 sun ji rauni a Kaduna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wani bom da ya fashe a kauyen Kidandan da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna ya yi sanadin mutuwar wani dalibin makarantar Islamiyya yayin da wasu goma suka samu raunuka.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya ce jami’an tsaro na gudanar da bincike a kan fashewar bom ɗin.

Advertisement

Batun Hana Lefe Neman Kawo Hargitsi  A Jihar Kano — Lauya

Aruwan ya ce, “A cewar rahotannin farko da aka samu daga kauyen da kuma jami’an tsaro, daya daga cikin daliban da ke karatu a karkashin wani malamin garin ya dauko wani abu daga daji, wanda daga baya ya fashe a tsakanin ‘yan uwansa dalibai.”

Ya ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar almajiri daya mai suna Zaidu Usman, yayin da wasu kimanin 10 suka samu raunuka kuma suna samun kulawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika-Zariya.

Advertisement

Aruwan ya ce, “Gwamna Uba Sani na jihar ya samu rahoton cikin kaduwa da bakin ciki, sannan ya aika sakon ta’aziyya ga wadanda abin ya shafa da iyalansu, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma basu lafiya.”

Ya ce gwamnan ya kuma yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su kara sanya ido kan ayyukan ‘ya’yansu a koda yaushe domin guje wa irin haka a gaba.

Advertisement

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending