Connect with us

News

Wani Jariri Ya Ɓata A Asibitin Waziri Gidado Da Ke Jihar Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wasu Rahotanni sun bayyana cewa an rasa wani Jariri dan kwana ɗaya da haihuwa a duniya a asibitin waziri gidado dake nan jihar  Kano.

Advertisement

An wallafa wannan labarin a shafin sada zumunta na Arewa Radio da ke Kano, inda suka bayyana cewa bayan mahaifiyar yaron ta haihu a gida a ranar Alhamis sai ta kamu da rashin lafiya, inda aka garzaya da ita asibitin domin kula da lafiyarta.

Bom ya tashi da wasu ‘Almajirai’ masu karatun islamiyya, ɗaya ya rasu, 10 sun ji rauni a Kaduna

Da misalin karfe 8 na dare tana cikin halin rashin lafiya wata mata ta dinga hilatar kakar yaron har ta tafi da jaririn nasu wanda kawo yanzu babu labarinsa.

Advertisement

Mahaifin yaron mai suna Aliyu ya ce, ya tafi sallah ya bar mahifiyar yaron da kakar yaron a asibiti sai dawo wa ya yi ake gaya masa yaron ya bata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending