News
Dakarun Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 43, sun kama 76 a Kudu maso Kudu
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda 43 sannan sun kama wasu 76 a yankin Kudu maso Kudancin kasar nan.
Jami’in yada labarai na rundunar Edward Buba ya bayyana sanarwar haka wa manema labarai ranar litinin.
Rabuwar Kawunan Yan Arewa Da Ake Samu Shi Ne Babban Abin Da Ke Kawo Koma —Malam Abba
Buba ya ce dakarun sun kama barayin man fetur 29 sannan sun ceto mutum 27 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce jami’an tsaron sun kama bindigogi 81, harsasai 2,150, motoci biyu, babura 25, wayoyin hannu 21, rediyo kirar baofeng 6 da kudi naira miliyan 1,266,920.00.
Bayan haka Buba ya ce dakarun sun lalata rijiyoyin mai 7, jiragen ruwa 13, tankin mai 23 da motoci 4 a yankin Neja-Delta.
Premium Times ta ruwaito cewa Sauran kayan da jami’an tsaron suka kama sun hada da murhun dafa abinci 15, na’auran tsatso mai 2 da matattar mai 16.
Dakarun sun Kuma kama lita 139,045 na bakin mai, AGO lita 25,115 da DPK lita 5,200.
