Connect with us

News

Cikakken Dalilin Da Yasa Aka Gurfanar Da Dan Bilki Kwamanda A Kotu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

An kama babban ɗan’adawar nan na jihar Kano Danbilki Kwamanda tare da tasa keyarsa zuwa gidan yari.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Tun da farko dai an gurfanar da Kwamanda bisa zargin yin wasu maganganu da ake zargin za su iya tunzura al’umma waɗanda suka shafi batun masarautun jihar Kano.

Yansanda Sun Karyata Jita-jitar Kai Harin Garkuwa Da Mutane A Jami’ar BUK

Rahotanni na nuni da cewa hukumar DSS ce ta fara gayyatarsa tare da miƙa ga shi ƴan sanda, kamar yadda Lauyan da ke kare shi Barriser Ibrahim Abdullahi ya tabbatar kafar yada labarai ta BBC hausa

Advertisement

“Ana zarginsa da yin wasu kalamai na tunzura jama’a kan batun masarautu a jihar Kano,” in ji shi.

Sai dai ya musanta zargin da ake ma sa a kotun.

Advertisement

Ya yi kalaman ne a wani gidan rediyo a Kano, bayan kalaman jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Musa Kwankwaso kan batun makomar masarautu a jihar ta Kano.

A cikin kalamansa da suka janyo kama shi, Danbilki ya ce ba za su yarda da cire sarakunan ba.

Advertisement

Kotu ta bayar da umarnin tafiya da shi zuwa gidan gyaran hali na Goron Dutse a Kano.

Sai a ranar 29 ga watan Janairu kotu za ta saurari buƙatar belinsa, kamar yadda lauyansa ya bayyana.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending