Connect with us

News

Bayan Shekaru 13 Ba Haihuwa Wata Mata Ta Rabauta Da Haihuwar Ƴan Shida

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Wata ƴar kasuwa mai suna Precious Ifeanyi shekarar ta 13 da aure bata taɓa haihuwa ba, kwatsam sai gashi Allah ya mata kyautar ƴan shida a ranar Litinin a Abuja.

Advertisement

Mrs Ifeanyi, wacce ta kasance ƴar asalin gseont Ebonyi da ke Ohaozara karamar Hukumar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarin Na Kasa NAN  a ranar Laraba a Abuja inda ta ke cewa ta haifi jariranta ras su shida, mata huɗu da maza ta hanyar Dashe wato”In-Vitro Fertilisation,’ IVF.

Da take ba da labarin yadda abin ya faru, Precious ta ce ta yi aure tun watanAfrilu 2010 kamar kowane mutum ta sa ran haihuwa bayan ɗan lokaci.

Advertisement

”Amma cikin ikon Allah haihuwa ya gagara; mun je asibitoci da dama mun kashe kuɗi amma shiru, Sai kawai muka haƙora muka zubawa Sarautar Allah ido.

“Sai ga shi yanzu, Allah cikin rahamarSa marar iyaka ya azurta mu,.”

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa Matar wacce ke cike da farin ciki ta shaida wa NAN cewa a cikin shekaru 13 da ta kwashe tana neman haihuwa, ita da mijinta, wanda ya kasance Fasto a Living Faith Church, Chikara a Jihar Kogi state, tace sun kashe maƙudan kuɗaɗe amma shiru.

Ta bayyana cewa shi ma mijin na ta ya yi matuƙar farin cikin samun haihuwar wannan ƙaruwar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending