Entertainment
Kotu a India ta bai wa mabiya addinin Hindu damar ibada a Masallachi
DAGA MAHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata kotu a kasar India ta bai wa mabiya addinin Hindu damar gudanar da ibadar su a wani Masallachi mai dimbin tarihi da aka gina shi a karni na 17 a birnin Varanasi.
Firaministan India narendra Modi lokacin da yake kaddamar da wani wurin ibadar Hindu a birnin Ayodha a ranar 22 ga wannan wata
Masallachin na Gyanavapi na daya daga cikin wuraren ibadar Musulmi da mabiya addinin Hindu dake samun goyan bayan jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ke kokarin kwacewa domin ganin sun dawo da shi karkashin mallakar su.
An dai gina wannan Masallachi mai dimbin tarihi ne a karni na 17 a karkashin mulkin Mughal, a garin da mabiya addinin Hindu ke amfani da fasahar ajiye gawarwakin su na dogon lokaci, kusa da kogin Ganges.
Kotun tace mabiya addinin Hindu na iya gudanar da ibada a Masallachin garin na Varanasi saboda yadda suka bayyana masa cewar an maye gurbin sa ne da wurin ibadarsu da ya rushe.
Alkalin kotun ya bukaci gwamnati da tayi wani tsari mai kyau a cikin kwanaki 7 masu zuwa, ta yadda mabiya addinin Hindun za suyi ibada a Masallachin.
Wannan hukunci na daga cikin takaddamar da aka dade ana yi a Gyanvapi, musamman ganin sanarwar hukumar binciken tarihin kasar India da ya bayyana cewar an taba samun wurin ibadar Hindu a wurin da Masallachin yake yanzu.
Masu tsatsauran ra’ayin addinin Hindu a sassan India na gabatar da irin wannan korafi a sassa da dama na kasar, inda suke cewa wuraren ibadar Musulmin da ake da shi a sassan kasar na matsayin wurin ibadar Hindu ne a can baya.
A makon jiya Firaministan Narendra Modi ya halarci wani kasaitaccen bikin bude wani katafaren wurin ibadar Hindu a birnin Ayodhya da aka gina bayan rusa wani Masallachi mai dimbin tarihi.
A shekarar 1992 mabiya addinin Hindu a karkashin jagorancin jam’iyyar Modi suka rusa wannan Masallachin, abinda ya haifar da rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 2,000 a fadin kasar, akasarin su Musulmi.