Entertainment
Kyautar Grammy Ta 2024: Fitattun Mawakan Najeriya Basu Yi Nasara Ba

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitattun mawakan Najeriya da suka hada da Burna Boy, Davido, Tems, Ayra Starr, Olamide, da Asake, basu yi nasara ba a Kyautar Grammy ta 2024.
Duk da yake an sa sunansu a fannonin tantance mawakan da suka yi fice a wake-wake, ba su samu nasara ba a ko guda ba.
Ba mu ne muka yi sanadin kaɗe saurayi da mota a Jibiya ba – Kwastam
A rukunin makakin da ya fi fice a fannin kade kade da raye raye- sun sha kaye a hannun mawakiyar Afirka ta Kudu.
Mawakiyar Afirka ta Kudu ta doke su inda wakar ta “Water” ta zama waka mafi shahara a Afirka, a kundin Grammy din.
Burna Boy, wanda ya sami lambar yabo ta fitaccen mawaki a duniya na shekarar 2021, ya sha kashi a wannan karon a hannun Shakti. Mawakan Indiya sun yi nasara da wakar su “This Moment,” inda suka doke Burna Boy da Davido.
Burna Boy ya zo a shirya domin yin daya daga cikin wakar shi da aka zaba a wurin bikin kai tsaye, sai dai bai samu yin hakan ba.