Entertainment
A Shirye Nake Na Aure Murja Kunya — Ibrahim Assalafi
Wani tsalelan Ustaz mai suna Ibrahim Assalafi dake zaune a unguwar burget ya mika kokin barar sa ga mahukunta dasu aura masa Murja Ibrahim Kunya tazo a matsayin uwar “ya”yan sa
Assalafi ya ce shi ba komai ne yaja hankalin saba illa yadda wannan baiwar Allah mai suna Murja Kunya take da wasu halaye masu kyau kamar yadda take fadar gaskiya hadi da rashin shiga abunda babu ruwan ta wadannan kadan kenan da suka ja gankalin sa har yasa ya kamu da kaunar ta
Ronaldo Ya Buga Wasa Na 1,000 A Tarihi A Karawarsa Da Al-Fayha Jiya Laraba
Ya kara da cewa shi ya bayyana muradin sa akan ta domin yayi jahadi wajan ganin ya zama sanadiyyar zaman ta matar aure
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Fitacciyar yar Tik Tok Murja Ibrahim Kunya ta bayyana cewa babu wanda ta ke so ta aura kamar Jaki.
Murja Kunya ta bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok kamar yadda Jaridar Inda Ranka ta samu kwafin bidiyo.
Haka zalika gwamnan Jihar Kano ya ce zai saka fitacciyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a cikin wadanda gwamnatinsa za ta yi wa auren zawarawa.
Gwamnan na jihar Kano ya kara da cewa gwamnatinsa za ta jawo mutane irin su Murja a jiki ba za ta wutakanta su ba kamar yadda wasu mutane suke yi.
