News
Jam’iyyar APC Ta Sha Kasa A Jigawa, Yakubu Na PDP Ya Yi Nasara A Zaɓen Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Duk da shirga-shirgan ayyukan da Gwamna Namadi yake rantamawa a faɗin jihar Jigawa, mutanen yankin Buji da Birnin Kudu sun wasa wa jam’iyyar sa ta APC ƙasa a Ido inda suka lallasa ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen ‘Inkonkulusib da aka gudanar a karshen mako.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana Yakubu Adamu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Birnin Kudu/Buji na ɗan majalisar tarayya da aka gudanar ranar Asabar.
Mazauna Minna Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Adawa Da Tsadar Rayuwa Tare Da Toshe Manyan Tituna
Kotun daukaka kara a watan Nuwamba, 2023, ta bayyana zaben 18 ga Maris, 2023 a Birnin kudu/Buji, a matsayin wanda bai kammala ba, sannan ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 8, guda bakwai a karamar hukumar Birninkuda (LGA) daya kuma a karamar hukumar Buji, domin tantance wanda ya lashe zaben.
Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in zaben Ahmad Baita ya ce Adamu na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 43,053, yayin da Magaji Da’u na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 42,544.
Baita ya bayyana cewa, kuri’un da kowane dan takara ya samu a zaben da aka sake an haɗa su da na zaben da aka yi a ranar 18 ga Maris, 2023 domin tabbatar da wanda ya lashe zaben.
Da yake jawabin samun nasara bayan sanar da sakamakon zaɓen Yakubu ya bayyana godiyarsa ga al’ummar yankin sa sannan ya yi alkawarin ya yi musu wakinci mai nagarta a majalisar Tarayya dake Abuja.
