Connect with us

News

‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 1 Bisa Zargin Yin Garkuwa Mutane Tare Da Kwato Shanu 55 A Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma barayin shanu, inda ta kwato shanu 55 a karamar hukumar Karaye.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Malam Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano ranar Litinin cewa, rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane ta kama wanda ake zargin.

Jihar New Jersey Za Ta Karbi Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya Na Shekarar 2026

Ya ce a ranar 4 ga watan Fabrairu da misalin karfe 05:40 ne aka kama wanda ake zargin mai garkuwa da mutane ne, na kauyen Kaya da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna da kuma karamar hukumar Karaye dauke da shanu 55

Wanda ake zargin ya amsa cewa sun gudu ne daga sansanin ‘yan bindigar Maidaro ta karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna bayan sun yi artabu da ‘yan bindigar, karkashin jagorancin Boderi Isiya na wannan adireshin.

Advertisement

Wanda ake zargin ya ce an kashe shugaban kungiyarsu na karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina tare da mataimakinsa a yayin fadan, sannan ya gudu da bindiga kirar AK-47 guda uku da shanu da dama, yana shirin zama a dajin karamar hukumar Gwarzo da Kareye.

Ya yi ikirarin cewa ya shiga hannu tare da wasu ‘yan sansanin a wasu hare-hare na garkuwa da mutane da satar shanu a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara.

A cewar Gumel, “Tun daga lokacin ne muka kaddamar da farautar ‘yan kungiyar da suka gudu.”

Gumel ya bada tabbacin aniyar ‘yan sanda na samar da tsaro ga ‘yan kasa tare da karfafa gwiwar mazauna yankin.

 

PRIME TIME

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending