News
Dole ne mu bi kadin abinda aka yi wa Jami’anmu —Hukumar KAROTA
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta kama daya daga cikin wadanda ake zargi da farwa Jami’anta
Hukumar ta sami nasarar kama matashin mai suna Saifullahi Haruna jim kadan bayan da wasu ɓata gari sun farwa Jami’an hukumar wadanda suke bincike ababen hawa a kan titin Panshekara cikin burnin Kano
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami in yada labarin na Hukumar Nabilusi Abubakar K/Na’isa ya turawa da Jaridar Inda Ranka
Sanarwar ta kara da cewa wasu ɓata garin matasa ne suka farwa Jami’an na KAROTA da misalin karfe 3 na dare a kan titin Panshekara cikin burnin Kano.
Hukumar ta ce ba za ta zuba ido ta kyale ana cin zarafin Jami’anta ba, domin kuwa aiki suke bisa tsarin doka
Tuni dai Hukumar ta miķa wanda ta kama wajen Baturen Yans. andan yankin da abin ya faru domin fadada bincike tare da daukar matakin kama ragowar domin gurfanar da su gaban sharia
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ya ce ya zama wajibi Hukumar ta mika godiyarta ga al’umma musamman wadanda suke ankarar da ita wani gyara idan buķatar hakan ta taso
Ya ce ķofar Hukumar a bude take ga duk wanda yaga wani gyara ko shawara ya sanar da Helkwatar Hukumar ta KAROTA ko ya same mu a kan Lambar Waya 08023608861 domin ciyar da aikin Hukumar da jihar Kano ta ɓangaren Sufuri gaba.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
