Connect with us

News

Babbar Magana: Wani Saurayi Ya Sare Kan Budurwarsa 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

An shiga rudani a yankin Riverain da ke Karamar Hukumar Sagbama a Jihar Bayelsa, yayin da wani saurayi ya sare kan budurwarsa.

Rahotanni na nuni da cewa babu cikakken bayani game da yadda lamarin ya faru, amma ta gano budurwar mai suna Maxuel Ebibraladei da saurayin nata Tony, sun haifi yaro a waje.

Dole ne mu bi kadin abinda aka yi wa Jami’anmu —Hukumar KAROTA 

 

Ana zargin saurayin ya kashe ta da misalin karfe 3 na daren ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewar mazauna yankin, sun cafke Tony tare da mika shi ga jami’an ‘yan sanda kafin ya tsere.

Advertisement

‘Yan sanda sun ajiye gawar marigayiyar a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa a jihar.

Tuni aka mika saurayin sashen binciken manyan laifuka na jihar (CID).

“Ba mu san abin da ya faru a tsakanin masoyan biyu da zai sa ya sare kan budurwarsa kuma uwar ɗansa ba.

“Su biyun sun kasance cikin zaman lafiya. Mun kasa tantance abin da ya faru,” cewar wani mazaunin yankin.

Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Musa Muhammed, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce rundunar za ta fitar da sanarwa kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending