Sports
Mbappe Zai Koma Real Madrid A Ƙarshen Kakar Bana
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗan wasan gaban PSG da Faransa, Kylian Mbappe ya amince zai koma taka leda a Real Madrid idan an kammala kakar bana.
Mbappe mai shekara 25 ya sanar da PSG cewar zai bar kungiyar da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen kakar watan Yuni.
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Bankado Badakalar Kudi A Wasu Hukumomin Gwamnatin Jihar
Duk da cewa har yanzu Mbappe bai kai ga cimma yarjejeniya ba da Real Maadrid, amma ana sa ran kungiyar za ta sanar da halin da ake ciki nan gaba kaɗan.
Mbappe shi ne kan gaba a ci wa PSG kwallaye, inda yake da 244 a raga, wanda ya lashe kofin duniya a tawagar Faransa a Rasha a 2018.
Mbappe ya bukaci a fayyace makomarsa kafin cikin watan Maris, wanda ya tattauna da shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi ranar 13 ga watan Fabrairu da cewar yana son komawa Real Madrid.
Bayan da aka san cewar Mbappe na son barin kungiyar tun ranar Alhamis, hakan ya sa ba a fara saka shi ba a gasar Ligue 1 ranar Asabar a wasa da Nantes.
Daga baya ya shiga karawar, wanda ya ci ƙwallo a bugun fenariti, tuni PSG ta bayar da tazarar maki 14 a kan teburin Ligue 1.
An ce ana sa ran zai amince da kunshin yarjejeniyar kaka biyar da zai ke karbar £12.8m a kowacce kakar tamaula.
Haka kuma Real Madrid za ta bai wa Mbappe £128m kudin rattaba ƙwantiragi da ladan wasa da sauransu da za a biya cikin shekara tara – sannan zai ke karbar kashi na tallace-tallacensa.
Tuni kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya fara tunanin wurin da zai ke saka Mbappe tare da Jude Bellingham da kuma Vinicius Junior.
Aminiya ta ruwaito cewa Luka Modric zai bar Real Madrid a karshen kakar bana, Mbappe ne zai karbi riga mai lamba 10, irin lambar da yake sa wa a PSG.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
