News
Sheikh Aminu Daurawa Ya Zama Malami Mafi Tarin Mabiya A Shafin Facebook
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Aminu Daurawa ya zama Malamin da ya fi kowanne Malami tarin mabiya a shafin Facebook a tsakankanin malaman addinin Musulunci da ke amfani da shafin a arewacin ƙasar.
Sheikh Aminu Daurawa wanda shi ne shugaban hukumar Hizba ta jihar Kano, ya kasance yana da mabiya guda Miliyan Ɗaya da Dubu Ɗari Huɗu kamar yadda binciken Yax Mokwa ya bayyana.
Tashin Kayan Masarufi Na Barazanar Durƙusar Da Kasuwanci A Kano —Yan Kasuwa
Yax Mokwa wanda ɗan asalin jihar Niger ne kuma mai yin sharhi akan al’auran yau da kullum ya gudanar da binciken ne a tsakanin fitattun malaman addinin Musulunci guda 15 da ke Arewacin Najeriya.
Jerin Malaman Addinin Musulunci Da Adadin Mabiyansu A Shafin Facebook
Jerin Malaman Da Aka Gudanar Da Binciken Akan su
Malaman sun haɗa da:
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Abdulwahab Abdallah
Sheikh Dr. Ahmad Mahmoud Gumi
Sheikh Ahmad Guruntum
Sheikh Bashir Aliyu Umar
Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya
Sheikh Kabiru Haruna Gombe
Sheikh Muhammad Nuru Khalid
Sheikh Ibrahim Maqari
Sheikh Muhammad Bin Usman
Sheikh Mansur Sokoto
Sheikh Ibrahim Saleh
Sheikh Mustapha Albarnawi
Sheikh Abdullahi Bala Lau
Tun lokacin da shafukan sada zumunta na zamani suka ɓullo jama’a ke amfani da su domin biyan buƙatu daban-daban.
Malamai da dama ne ke rungumar shafukan sadarwa na zamani domin isar da sakonni ga mabiyansu da kuma aikewa da nasihohi da fadakarwa ta hanyar wallafa ayoyin Al-Kur’ani da hadisan Manzon Allah, Annabi Muhammadu (S.A.W) da kuma fahimtar malamai a kan matsalolin rayuwa da yadda za a shawo kan su.
