News
Tashin Kayan Masarufi Na Barazanar Durƙusar Da Kasuwanci A Kano —Yan Kasuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gamayyar shugabannin ƙungiyoyin ‘yan kasuwar Kano da suka yi wani gangami da kira da gwamnatin Bola Tinubu sun shawarci gwamnatin Njeriya da ta ɗauki matakin gaggawa ko kuma kasuwanci ya durkushe gabaki ɗaya a Nijeriya musamman a wannan lokaci da dala ta haura Naira 1500 kuma ta ke ta hauhawar kamar motar da birkin ta ya tsinke ana gudu a 180 na ma’aunin tuƙin mota.
Gamayyar ƙungiyoyin na shugabannin ‘yan kasuwar Kano kimanin 30 da suka yi gangami a taron da suka gabatar a ranar Lahadi da ta gabata ƙarƙashin shugabancin shugaban gamayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwan Alhaji Junaidu Muhammad Zakari ya samu halartar ɗaukacin shugabanin ƙungiyoyin da ke kasuwanin Kano daban-daban da kuma gabatar da jawabai daga bakunansu a wannan gangami na ‘yan kasuwa da ya gabata a ranar Lahadi a birnin Kano.
Wasu Fasinjojin Jirgi Sun Gudanar Da Zanga – zanga Kan Jinkirta Tashin Jirgi A Jihar Kano
Kaɗan daga cikin shugabannin qungiyoyin da suka halarta akwai Alhaji Sani Salisu Dada shugaban ƙungiyar ‘yan canji na ƙasa reshen Jihar Kano sai kuma Shugaban qungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari Alhaji Balarabe Tatari haka akwai Alhaji Ali Isa Musa wakilin ‘yan Chana a Kano haka kuma akwai Alhaji Malanta daga babban mayanka Kano Abba Tuwa shugaban ƙungiyar mahauta ta ƙasa reshen Jihar Kano.
Kazalika akwai Alhaji Yau Karas shugaban ƙungiyar kasuwar Kurmi Kano, da dai sauran shugabannin ƙungiyar da suka zo daga kasuwar ‘yan Lemo, da sauransu waɗanda dukkaninsu sun nuna takaici da damuwa kan yadda kayan masarufi da kayan abinci suka fi ƙarfin mafiya yawan ‘yan Nijeriya, inda suka buƙaci shugaban ƙasa da gwamnonin Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaji su ɗau mataki a kan wannan babbar matsala da ke neman gurgurta tattalin arziƙin Nijeriya.
A ƙarshe Alhaji Junaidu Muhammad Zakari, shugaban gamayar ƙungiyoyin ‘yan kasuwar na Kano sama da 30 ya ce sun rubuta takarda ga Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da shugaban ƙasa da ɗaukacin masu ruwa da tsaki na Kano da Nijeriya baki ɗaya kan kawo ƙarshen wannan matsala da ta damu al’ummar Nijeriya.
