Connect with us

News

Hukumar NDLEA ta kama tarin makamai da hodar Iblis a gabar ruwan Najeriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya sun chafke wasu mutane mambobin wata kungiya dake hada-hadar miyagun kwayoyi da muggan makamai tsakanin kasashen Africa.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai, Femi Babafemi ta ce an kama mutanen da hodar Iblis mai nauyin kilogram 1,044 sai kuma tarin muggan makamai da alburusai.

Advertisement

Sheikh Aminu Daurawa Ya Zama Malami Mafi Tarin Mabiya A Shafin Facebook

Bayanai sun ce mutanen sun sauka a tashar ruwa ta Tincan Island dake Lagos, bayan tasowar su daga garin Durban na Africa ta kudu.

Mutanen da aka kama sun hadar da Falowo Samuel Kayode wani ma’aikacin jirgi da kuma Anjorin Idowu da Uzairu Ahmed Iguda, wanda dukannin su ma’aikatan tashar jiragen ruwan ne.

Advertisement

Bayanan farko-farko da mutanen suka bayar ya taimaka wajen kamo wani Mohammed Mukhtar Sule, wanda yake jiran su a Najeriya, don taimaka musu wajen rarraba kayan laifin.

Sanarwar hukumar ta kara da cewa tun tasowar su daga Africa ta kudu ta sami labarin irin kayan Laifin da suka dauko don haka ta shirya jami’an ta da suka yi ram da su ba tare da bata lokaci ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending