Connect with us

News

Idan aka kai wa masu zanga-zanga farmaki, za mu tsayar da komai cak a Najeriya —Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta ce ta na da masaniyar cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki sojojin-hayar wasu zauna-gari-banza domin su kai wa mambobin NLC hari idan suka fita zanga-zanga a ranar Talata da Laraba.

NLC ta tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa idan aka kuskura wasu zauna-gari-banza suka afka wa masu zanga-zanga, to za su bada umarnin gaba ɗaya kowa ya tafi yajin aiki, komai ya tsaya cak, tattalin arzikin ƙasa shi ma ya yi tsayuwar-gwamin-jaki.

Advertisement

Kungiyar NLC ta zargi gwamnatin tarraya da kitsa kai wa ‘ya’yanta hari a lokacin zanga-zanga a faɗin Najeriya 

“Idan aka kai mana hari, to komai zai tsaya cak a ƙasar nan. Ma’aikata za su daina zuwa aiki. Kada ma a yaudari kowa, mu da sauran ‘yan Najeriya da aka gasa wa raɗaɗin tsadar rayuwa fa ba wanda ya isa ya yi mana wata barazana,” cewar Shugaban NLC, Joe Ajaero, cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Ajaero ya bayyana sunan gungun wasu da ya kira ‘yan ta-kifen da gwamnatin tarayya ta kafa cikin gaggawa, ta ke kashe masu kuɗi domin kawai su hargitsa waɗanda za su fita zanga-zangar lumana a ranakun Talata da Laraba. Za su fita zanga-zangar nan saboda yunwar da aka ƙaƙaba mana.”

Advertisement

PREMIUM TIMES ta bada labarin cewa NLC ta shirya fita zanga-zangar lumana a ranakun Talata da Laraba, wato 27 da 28 ga Fabrairu, saboda raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shi a faɗin ƙasar nan.

Gwamnatin Tarayya dai na ta roƙon NLC kada su tafi yajin aiki, domin a cewar ta, ta na bakin ƙoƙarin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da shine.

Advertisement

Amma a ranar Lahadi Shugaban NLC ya ce ba gudu ba ja da baya, za su yi zanga-zangar lumana a ranakun Talata da Laraba. “Kuma ba a magance yunwa ko matsalar tattalin arzikin ƙasa ta hanyar dankwafe masu zanga-zangar lumana.” Inji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending