Entertainment
Kotu Ta Haramtawa Ado Gwanja Yin Waƙa, Bayan Kama Shi
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Babbar kotun jihar Kano Mai Lamba biyar karkashin jagorancin Mai Sharia Aisha Mahmud ta bada umarnin a kamo mata mawaƙi Ado Isa Gwanja.
Rahotanni na nuni da cewa Kotun ta kuma haramta masa waka har sai yan sanda sun kammala bincike a kansa.
Idan za’a iya tunawa a bara lokacin da mawakin yayi wata waka mai suna “WAR” zauran malaman kano sun shigar da shi kara a kotun Shari’ar Musulunci dake Bichi ta hannun lauya Barr. Sulaiman Gandu, saboda a cewar su wakar akwai kalaman batsa a cikinta kuma zata iya bata tarbiyyar yara a Kano.
A wancan lokacin kotun ta bada izini a kamo mawaki ado Gwanja, amma sai ya garzaya babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba biyar ya kuma karɓo takardar da ta hana kotun ta kama shi a wancan lokacin.
A zaman ta na wannan rana kotun karkashin jagorancin mai Shari’a Aisha Mahmoud ta bada umarnin a kama Ado Gwanja, sannan ta ce ta haramta masa yin kowacce irin waka har sai an yan sanda sun kammala bincike kan zargin da malaman kano suka yi masa.
Haka zalika kotun ta ce ta haramtawa Ado Gwanja zuwa gidan biki don yin waka, sannan kuma ta hana wani ko wata ya hau wakar sa a dandalin sada zumunta.
Kotun ta ce duk wanda ya hau wakar kafin a kammala wannan Shari’ar to su sani sun karya doka kuma kotu zata sa a Kamo su.