News
Gwara na mutu da wannan rayuwar matsi da muke ciki”
DAGA MUBARAKA BALA IDRIS
Tsadar rayuwa na ci gaba da tilastawa ‘yan Najeriya shiga yanayin da ba su taba tunani ba, inda yanzu suke cin abincin da a baya ko dabbobi ba za a bai wa ba,
A yanzu haka, sakamakon tsadar shinkafa, mutane kan sayi wata shinkafa da ake kira ‘Afafata’ wadda ta yi kama da damajin kamfani.
Wata mai jego mai cin shinkafar ta ce gwara ta mutu da ta ci gaba da zama cikin matsin rayuwa.
“Wallahi indai zan samu rahamar Allah na gwammace na mutu da wannan rayuwar da muke ciki. Wannan rayuwa ai mutuwarka ce ta fi sauki.”
Ana dai sayar da kwanon shinkafa nau’in afafata kan naira dubu daya da dari takwas sabanin lafiyayyar shinkafa wadda ta farashinta ya wuce.
Mai jegon ta ce a hakan ma sai dai su sayi gwangwani sannan kuma mutum zai kwashe awa biyu zuwa uku kana tsince datti.
“Kana ci za ka ji daci a bakinka.Wallahi ba na iya cinta.”
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
