News
Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya na zanga-zanga kan matsin rayuwa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A yau ne ƙungiyoyin kwadago a Najeriya ke zanga-zanga saboda tsadar rayuwar da al’umma ke fuskanta a ƙasar.
Ƙungiyar kwadagon ta ce za ta yi zanga-zangar ne na yini biyu – Talata da Laraba.
Hauhawar farashi a ƙasar wadda tattalin arzikinta shi ne mafi girma a Afirka ya kai kusan kashi 30 cikin 100 yayin da darajar naira ke ci gaba da karyewa.
Dalilan cire wa Nijar, Mali da Burkina Faso takunkumi – Kungiyar ECOWAS
Matsalar rashin wuta na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta’azzara halin matsin da ake ciki a ƙasar.
Bankin raya ƙasashen Afirka AfDB ya yi gargaɗin cewa halin da ake ciki na iya janyo bore a ƙasar duk da cewa tuni wasu jihohin ƙasar suka yi makamanciyar zanga-zangar ta tsadar rayuwa.
Gwamnati ta ce za ta rage kuɗin da take kashewa wajen tafiyar da harkokinta sannan ta yi alƙawarin ɗaukan matakai domin taimakawa al’umma da kuma masu ƙananan sana’oi.
Babu bayanai kan yawan ma’aikatan da za su shiga zanga-zangar saboda mutane da dama na zargin ƙungiyoyin da rashawa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
