News
Ƴan sanda Sun Saka Ladan Miliyan 50 Dan A Nemo Wasu Ƴan Bindiga
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yansanda a jihar Katsina ta sanya ladan miliyan 50 kan wasu ‘shugabannin ‘yan fashi’ guda biyu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar Asp Abubakar Sadiq ya fitar, ta ce duk wani wanda zai taimaka da bayanai da za su kai kamo shugabannin ƴan fashin masu suna ‘Modi Modi’ da kuma ‘Jan Kare’ zai samu ladar miliyan 50.
Kuskurene gwamnan jihar Kano ya baiwa daurawa hakuri cewar (BABA IMPOSSIBLE)
Asp Abubakar ya ce ƴan fashin sun kasance suna cin karensu babu babbaka a jihar ta Katsina, musamman ma yankuna da ke ƙananan hukumomin Kankara da kuma Safana.
“Samar da tsaro na da muhimmancin gaske, shi ya sa gwamnatin jihar Katsina da ƴansandan jihar da kuma sauran hukumomin tsaro suka ɗauki aniyar magance duk wasu masu tayar da zaune tsaye da hana zaman lafiya a faɗin jihar,” in ji Asp Abubakar.
Ya ƙara da cewa sun yi tayin bayar da ladan kuɗin ne a ƙoƙarinsu na ganin an yi wa mutane adalci, ganin cewa batun tsaro hakki ne da ya rataya wuyan kowa.
Ya kuma ce hakan zai sa a kawo karshen ayyukan ɓata-gari a jihar.
Kakakin ƴansandan ya ce rundunar na kira ga kowane ɗan jihar da ya zo ya gabatar da bayanai da za su taimakawa jami’an tsaro wajen kama waɗanda ke sahun gaba a yin garkuwa da mutane da kuma fashi.
