News
Mai POS Ya Mayar Da N10m Da Wani Kwastomansa Ya Tura Masa Bisa Kuskure A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani mai sana’ar POS a jihar Kano ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa yayin da yake son tura masa naira dubu 10, kamar yadda rundanar ’yan sanda reshen jihar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a watan Disamba na shekarar 2023 lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karɓi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.
Daga nan ne sai mai POS ɗin ya garzaya hedkwatar ƴan sanda da ke jihar Kano kuma ya sanar da su abin da ya faru. Sai ƴan sandan suka dauki bayansa kuma suka bukaci ya ba su lokaci don su gudanar da binciken gano mutumin da ya tura masa makudan kudin bisa kuskure.
Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce bincike ya kwashe su kimanin wata uku kafin su yi nasarar gano mutumin wanda dan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.
Rundunar ’yan sandan ta ce tuni mai POS din ya mayar wa dan kasuwan kudinsa wato naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in (9,990,000:00). Jin dadin haka ya sa dan kasuwan ya ba mai POS din kyautar naira 500,000. Kazalika rundunar ’yan sandan ta yaba da kyakkyawan halin mai POS din kuma ta bukaci sauran jama’a da su yi koyi da shi.
A kwanakin baya ma an samu wani dan agaji mai suna Salisu Abdulhadi wanda ya tsinci naira miliyan 100 a jihar Katsina kuma ya yi cigiyarsu har sai da aka gano ainihin mai kudin, inda aka mayar masa da kudinsa
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
