News
Shugaba Tinubu Ya Nemi Gwamnonin Jihohi Da Su Yi Watsi Da Sabanin Siyasa Su Hada Kai Wajen Gina Kasa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su yi watsi da sabanin siyasa su hada kai da gwamnatin tarayya wajen gina kasa.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a lokacin buda baki tare da gwamnoni a fadar gwamnati da ke Abuja, a jiya Alhamis.
Ana Zargin Wani Mutum Da Kashe Mijin Ƙanwarsa Kan Gishirin N20 A Jihar Kano
Ya kuma jaddada muhimmancin a jiye siyasa a gefe a fuskanci shugabanci, inda ya ce akwai bukatar hadin kai kai a tsakanin masu ruwa da tsaki.
Da yake karin haske kan muhimmancin watan Ramadan Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da lokutan wajen yin addu’o’i, da kuma sadaka.
Shugaban ya bayyana kwarin guiwar samun mafita mai dorewa a nan gaba, inda ya ce gwamnatin sa na iya bakin kokartinta wajen shawo kalubalen da kasar nan ke fuskanta. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa bayarda umurnin raba hatsi da ya kai tan 42,000.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
