Connect with us

News

Ana Zargin Wani Mutum  Da Kashe Mijin Ƙanwarsa Kan Gishirin N20 A Jihar Kano

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wani magidanci mai suna Zakari Hamza mai shekara 45, ya gamu da ajalinsa a hannun ɗan uwan matarsa, mai suna Magaji Salisu saboda karbar bashin gishiri na Naira 20.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa dan marigayin, Ibrahim Zakari, ya ce rigima ce ta kaure tsakanin mahaifinsa da kanin matarsa, lamarin da ya kai ga mutuwar mahaifinsa.

Hukumar EFCC ta ɓallo wa Yahaya Bello ruwan zafi, ta saka sunan sa cikin harƙallar kuɗaɗen da aka gurfanar da ƙanin sa

Ibrahim ya ce, an samu saɓanin ne a lokacin da mahaifinsa ya dawo daga kasuwa, sai matarsa Sadiya Salisu ta shaida masa cewa ta karɓi bashin gishiri na naira 20, lamarin da ya fusata mahaifinsa da a baya ya yi gargaɗi game da karɓar kowane irin bashi daga wurin kowa.

Advertisement

Ibrahim ya ce rigimar da ta faru tsakanin marigayin da matarsa ta kai ga yin musayar kalamai.

Ɗan ya ce mahaifinsa ya koma shagonsa ya kira ƙanin matarsa a waya ya shaida masa duk abin da ya faru a gida tsakaninsa da matarsa.

Advertisement

An yi zargin cewa ɗan uwan matar ya fusata ya zo gidan yana neman mijin ‘yar uwarsa, amma bai same shi a gida ba.

Daga nan ne ya yanke shawarar ya bi shi zuwa shagonsa da ke ‘Yan shinkafa a Karamar Hukumar Kura ta Jihar Kano.

Advertisement

Ɗan marigayin ya ƙara da cewa, nan take Magaji yana yin arba da mahaifinsa, sai ya fara dukansa har ya kai ga ƙashin ƙirjinsa ya karye.

Ya ce sun kai mahaifinsu wani asibiti da ke kusa da garin Kura inda likita ya yi masa magani ya sallame shi, amma bayan komawarsu gida sai mahaifinsa ya rasu.

Advertisement

Ibrahim ya ce sun kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda kuma jami’in ‘yan sanda na Kura ya gayyaci matar da ɗan uwanta kuma yanzu haka ana bincike a kan lamarin.

Ya roƙi kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano da ya tabbatar wa mahaifinsa adalci.

Advertisement

Ya zuwa lokacin tattara rahoton babu wani martani daga rundunar ‘yan sandan jihar ta yi a kan lamarin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending