News
DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu ta yanke wa dan China da ya kashe budurwarsa ƴar Kano hukuncin kisa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa Geng Quandong, ɗan ƙasar China da ya kashe budurwarsa Ummukulsum Buhari hukuncin rataya.
Kotun ta samu Quandong da laifin kisan Ummukulsum, wacce aka fi sani da Ummita, laifin da ya saɓawa sashi na 221 na kundin dokokin laifuka na jihar Kano.
Wannan dalili ne ya sanya kotun ta yanke wa Quandong, mai shekaru 47 hukuncin kisa.
A tuna cewa a ranar 16 ga watan Satumbar 2022 ne Quandong ya caccaka wa budurwar tasa Ummita wuka har ta ce ga garinku nan a gidan su da ke unguwar Jambulo a Kano.