News
Gwamnan Kano Ya Bada Tallafin Naira Dubu 500 Ga Maniyyata Aikin Hajjin Bana Da Suka Fito Daga Kano.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da tallafin Naira 500,000 ga kowanne maniyyatan da za suyi aikin hajjin shekarar 2024 a kasar Saudiyya.
Wata majiya mai tushe a hukumar alhazai ta Kano ta shaida wa jaridar Peoplespen24 a ranar Laraba.
Cikakken Dalilin da Yasa Gwamnan Kano Zai Samar da Sabbin Ma’aikatu a Jihar
Wannan sanarwar ta zo ne a matsayin wani gagarumin tallafi ga maniyyata bayan da hukumar alhazai ta najeriya (NAHCON) ta buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.
Gwamnatin jihar Kano ta ce maniyyatan da suka yi rajista kuma suka biya kudaden ajiya na farko na Naira miliyan 4.7 da kuma N4. Miliyan 5 da hukumar alhazai ta jiha yanzu za su saka Naira miliyan 1.4 daga cikin N1. 9 miliyan da ya karu.