News
Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Haramta Zirga-zirga A Tsakanin Iyakokinta Da Katsina Da Sokoto Daga Karfe 7 Na Yamma
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe 7:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe a kan iyakokin jihar da ke makwabtaka da jihohin Katsina da Sokoto.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Manir Haidar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Gusau ranar Talata.
Shugaban Senegal Ya Naɗa Ubangidansa Sonko A Matsayin Firaiministan Kasar
Haidara ya ce, an yanke wannan hukuncin ne a yayin taron kwamitin tsaro na jihar.
Ya ce, “Ya zuwa yau, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin hana zirga-zirga a kan iyakarta da garin ‘Yankara da ke jihar Katsina da kuma iyakar Bimasa ta jihar Sokoto daga karfe 7:00 na dare zuwa 6:00 na safe kullum.
“An yanke wannan hukuncin ne don magance matsalar sace-sacen matafiya a kan babbar hanyar Sokoto zuwa Gusau zuwa Funtua.
“Wannan wani bangare ne na matakan da gwamnatin jihar ke dauka na ragewa tare da magance ayyukan sace-sacen da ‘yan bindiga ke yi, musamman a manyan titunan jihar,” in ji shi.
A cewar kwamishinan, an umurci dukkan masu ababen hawa da matafiya da su bi umarnin gwamnati.
“An umurci hukumomin tsaro da su sanya ido kan iyakokin biyu tare da tabbatar da cikakkiyar bin doka,” in ji shi.