News
Shugaban Senegal Ya Naɗa Ubangidansa Sonko A Matsayin Firaiministan Kasar
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sabon shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya naɗa shugaban babbar jam’iyyar adawa, Ousmane Sonko a matsayin firaiministan ƙasar.
Ousmane Sonko dai shi ne ubangidan shugaba Faye a harkokin siyasa kuma an ɗaure su a gidan yari daf da zaɓen na watan Maris.
Jaridar Inda Ranka ta taya Babban Editan ta murnar cika shekara 25
Amma daga bisani tsohon shugaban ƙasar Macky Sall ya yi masu afuwa, tare da wasu fursunonin siyasa.
Bayan ƴan sa’o’i kaɗan da hawansa mulki a matsayin shugaban ƙasar Senegal ne shugaba Faye ya naɗa Sonko a matsayin firaiminista,” fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na X.
Tun da farko dai an bayyana Sonko a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa amma bayan an kama shi ne sai aka yanke masa hukuncin cewa bai cancanci tsayawa takara ba – matakin da ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.
A jawabinsa na rantsar da shi a ranar Talata, shugaba Faye ya ce Senegal za ta zama ƙasa mai babban fata tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
