News
Mutum aƙalla 21 ne suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a jihar Kogi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mutum aƙalla 21 ne suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, a cewar shaidu.
Edibo Ameh Mark, shugaban ƙaramar hukumar Omala, inda lamarin ya faru, ya ce an binne mutanen da aka kashe.
Sharuɗɗa 8 da ke tattare da Lamunin Kuɗin Karatun Ɗaliban Gaba Da Sakandare
Ya ƙara da cewa Fulani ne suka kashe mutanen a wani harin ramuwar gayya da suka kai bayan mazauna ƙauyen sun kashe ƴan’uwansu guda shida kwana uku da suka wuce, ciki har da biyu da aka fille wa kawuna.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya na ci gaba da barazana a yankin saboda ƙaruwar rashin wuraren kiwo da a wasu lokuta kan sa makiyaya su shiga gonakin al’ummar gari.
“Ba mu taɓa tunanin za a kawo wannan hari ba,” in ji Elias Atabo, mai shekara 54. “Maharan sun kwashe fiye da minti 45 suna harbe-harbe.”
Wani mazaunin yankin mai suna Atabor Julius ya ce makiyaya kusan 100 ne suka kai hari a ƙauyensu ranar Alhamis inda suka riƙa yin harbi na kan mai-uwa-da-wabi, yana mai cewa sun gano gawarwaki 19 a lokacin da lamarin ya faru sannan aka gano ƙarin gawawwaki 15 ranar Juma’a.
Julius ya ƙara da cewa yawancin mutanen da suka mutu tsofaffi ne da ba za su iya guduwa ba.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar bai ce komai ba game da batun duk da saƙon da aka aika masa.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
