Connect with us

News

Sharuɗɗa 8 da ke tattare da Lamunin Kuɗin Karatun Ɗaliban Gaba Da Sakandare 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sa wa dokar kafa Hukumar Bada Lamuni ga Ɗaliban Manyan Makarantu hannu, bayan an yi wa dokar gyare-gyaren da suka wajaba.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu, wadda ke ɗauke da sa hannun Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, an bayyana gyare-gyaren da aka yi wa dokokin, waɗanda suka haɗa da:

Jamiyyar NNPP ta sauya tambarin ta (Logo) daga kayan Marmari zuwa hoton littafi

1. Duk wanda ya bayar da bayanan ƙarya wajen cika fam ɗin neman lamunin gwamnatin tarayya, to ya aikata laifin cin amanar ƙasa, kuma hukuncin ɗaurin shekaru 3 a gidan kurkuku zai hau kan sa.

Advertisement

2. Hukumar Bada Bashi ga Ɗalibai (NALDAFUND), za ta iya yafe bashi ga ɗalibin da rai ya yi halin sa bayan ya karɓi bashin. Ba za a tilasta iyayen sa su biya ba.

 

Advertisement

3. Ɗalibin da aka bai wa ramcen zai iya neman a ƙara masa wa’adin lokacin biyan kuɗin, matsawar ya je kotu ya karɓo kwafen rantsuwar cewa har yanzu bai samu aikin da ya fara samun kuɗi ba, tun bayan kammala aikin NYSC da ya yi.

 

Advertisement

4. NALFUND za ta fara neman ɗalibi ya biya kuɗin da ya karɓa bayan shekaru biyu da kammala NYSC.

 

Advertisement

5. Idan ɗalibi ya nemi ramcen kuɗin da zai biya kuɗin karatu, to NALFUND za ta biya kuɗin a sasusun banki na makarantar ne. Amma idan ramcen kuɗin ɗawainiyar faɗi-tashin karatun sa ne, to a na sa asusun bankin za a tura masa.

 

Advertisement

6. Ba za a hana ɗalibi ramcen ba, ko da kuwa gwamnatin tarayya ta na bin mahaifin sa bashi.

 

Advertisement

7. An cire sharaɗin sai ɗalibi ya bada sunan mutumin da zai tsaya masa a wurin karɓar bashin. Muddin aka tantance shi, za a ba shi lamunin kawai.

 

Advertisement

8. An cire sharaɗin sai hukuma ta ɗan adadin ƙarfin arziki ko ƙarfin talaucin iyayen ɗalibi kafin a ba shi ramcen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending