News
Lallai a tsara yadda za a rika saka ɗaliban jami’ar ‘Tafi Da Gidan Ka’ NOUN shirin NYSC – Umarnin Shugaba Tinubu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci ma’aikatar ilimi ta tsara yadda za a saka ɗaliban da suka kammala karatun digiri daga buɗaɗɗiyar Jami’a ko kuma ‘jami’ar tafi da gidan ka’ wato NOUN tsarin yi wa kasa hidima, NYSC.
Shugaba Tinubu ya fadi haka ne a taron yaye daliban Jami’ar karo na 13 da aka yi a karshen makon jiya a Abuja.
Da Dumi Dumi: Gwamnatin Jihar Kano ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kansa
Premium Times ta ruwaito cewa a shekarar 2018 tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dokar NOUN da aka yi wa kwaskwarima domin bai wa jami’ar damar gudanar da ayyukanta kamar sauran jami’o’in Najeriya tare da gain cewa daliban da suka kammala karatun kwas din shari’a sun samu damar zuwa makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya (NLS) da kuma shiga NYSC.
Makarantar koyan aikin lauyan NLS ta fara amincewa da dalibai daga jami’ar NOUN a shekarar 2022 amma har yanzu basu yi aikin yi wa kasa hidima ba.
Shugaba Tinubu Wanda Shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC Biodun Saliu ya wakilta a taron ya ce lallai ya kamata a shigar da wannan tsari cikin gaggawa domin ɗaliban da suka kammala karatu su yi NYSC.
Da ga nan sai ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da maida hankali wajen bunƙasa ilimi a kasar nan.
