News
Uba Da Dansa Tare Da Wani Dan Kai Dauki Sun Rasu A Kokarin Dauko Wata Wayar Hannu Data Fada Cikin Shadda A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Uba da Dansa tare da wani dan kai dauki sun rasu a kokarin dauko wata wayar hannu data fada cikin Shadda a garin Yar Gwanda dake karamar hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.
Tunda farko al’amarin ya faru ne, lokacin da mutumin Mai suna Malam Danjuma Black, ya je bandaki biyan bukata, to sai wayarsa ta fada cikin Shaddar, Ashe ashe ajali ne ke kira.
Hauhawar Farashi Ta Sake Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 10 Cikin Talauci – Bankin Duniya
Ganin haka tasa mutumin ya dauko tsani da zummar dauko wannan waya, ai kuwa shigarsa ke da wuya, ya kasa fitowa, kasancewar masan dama can tsohuwar rijiya ce, nan da nan aka kirawo dansa wanda matashi ne aka sanar da shi halin da ake ciki, abunka da soyayyar Da da mahaifi, sai kawai ya shiga wannan masai domin kaiwa mahaifinsa dauki, ashe shima ajali ne ke kiransa, shima ya kasa fitowa.
Ganin haka tasa aka kirawo wani mai harkar ginin rijiya tunda dama ya saba da irin wannan aikin, domin ya kai masu daukin gaggawa.
Da farko ya shiga cikin Shaddar harma ya samu nasarar dauko Dan Marigayin ya fito dasu amma baya motsi, sai kuma ya kara komawa ciki domin dauko Malam Dan juma Wanda shi ne mahaifin matashin, to bayan ya yi yunkurin dauko shi domin fitowa, harma ya fara yo sama, sai shima ya yanke jiki suka sake fadawa cikin Shaddar tare.
Ganin haka Yan garin suka yi gaggawar neman daukin Jami’an kashe gobara, kasancewar an rasa wanda zai iya shiga ciki.
Bayan dauko da jami’an kashe gobara suka yi aka garzaya dasu zuwa Babban Asibitin Bichi, Kuma a nan ne aka tabbatar da rai ya yi halinsa su duka ukkun.
Tuni aka yi masu sutura kamar yadda addinin musulunci ya yi tanadi, kamar yadda Mazaunin garin Sani Isma’il Yar Gwanda ya shaida man.
