Connect with us

News

Mutum 10 Sun Mutu A Lokacin Da Wasu Jirage Masu Saukar Ungulu Su Kayi Karo Da Juna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Mutane 10 suka mutu a lokacin da wasu jirage masu saukar ungulu na sojojin Malaysia biyu sun yi karo da juna, yayin wani atisaye da suke yi a yau Talata.

Babban jami’in gudanarwa na hukumar kwana-kwana da aikin ceto ta kasar, Suhaimy Mohamad Suhail ne ya tabbatar da faruwar lamarin kamar yanda Radiyon Faransa ta ruwaito

Advertisement

Yau Shugaba Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Kasashen Netherlands Da Saudi Arabia

Firaministan kasar Anwar Ibhrahim ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hadarin da ya bayyana a matsayin mai tada hankali, inda ya ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin faruwansa.

An gayamin cewar ma’aikatar kula da harkokin tsaro za ta gudanar da bincike, musammanma rundunar sojojin ruwa ta kasa TLDM, don gano musabbabin farun hadarin.

Advertisement

Ba kasafai aka cika samun aukuwar hadarin jiagen sama masu saukar ungulu a kasasshen da ke shiyar Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya ba.

Amma a watan da ya gabata, wani jirgin sama mai saukar ungulu na jami’an da ke tsaron gabar ruwan Malaysia yayi hadari a mashigar Malacca, duk da dai ba a samu asarar rai ba.

Advertisement

Haka nan a shekarar 2016, akwai mataimakin ministan kasar da ya rasa ransa a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a jihar Sarawak da ke kasar

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending